Kwamitin sulhu ya kuma jaddada bukata ga bangarorin kasa ta Libya da su aiwatar da yarjejeniyar siyasa nan take, da kuma kafa gwamnati na hadin kan al'ummomin kasa, ta yadda za a iya dukufa cikin hadin gwiwa wajen yaki da kungiyoyin ta'addanci na kasa da kasa da kuma fuskantar kalubalolin da kungiyoyin suka haifar wa kasar sakamakon kwashewar albarkatun da suka aiwatar a kasar.
Haka kuma, kwamitin sulhu na MDD ya nuna damuwarsa dangane da kalubalolin da kungiyar IS da kungiyoyin dakaru da suka sanar da goyon bayan su ga IS da mabiyan ta suka haifar wa kasar Libya wajen shimfida zaman karko a kasar, shi ya sa, kwamitin sulhu na MDD ya jaddada cewa, ya kamata a dauki matakan yin rigakafi da kuma hana wadanda za su samar da kudade ga masu aikata laifuffukan ta'addanci.
A ran Alhamis 7 ga wata, wani ya kai hari ta fasa boma-boman da aka dasa cikin wata mota, bayan da ya tuka motar cikin wata sansanin horas da 'yan sanda dake birnin Zlitan dake yammacin kasa ta Libya.
Bisa labarin da aka samu a ranar Jumma'ar nan, an ce, harin ya riga ya hadddasa rasuwar mutane guda 70, yayin da sama da dari suka jikkata. Kana, a ranar Alhamis, reshen kungiyar IS dake Libya ya sanar da daukar alhakin harin. (Maryam)