Babban magatakardan MDD Ban Ki-moon dake ziyara a kasar Tunisiya ya yi kira ga gwamnatin hada kan al'ummar kasar Libya da ta koma Tripoli, babban birnin kasar a jiya Talata, domin fara karbar mulkin kasa lami lafiya.
Ban Ki-moon ya ce, in hali ya yarda, ya kamata gwamnatin Libya ta yi iyakacin kokarin dawowa birnin Tripoli domin gudanar da harkokin kasar, kuma ya kamata majalisar wakilan jama'ar kasar ta dauki nauyinta wajen tabbatar da yarjejeniyar siyasa a wannan kasa da ke fama da rikici. (Lami)