in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta tsawaita wa'adin aikin tawagar musamman a Libya
2016-03-16 09:30:15 cri
Kwamitin sulhu na MDD ya tsaida kudurin a Talatar data gabata cewa, zai tsawaita wa'adin aikin tawagar musamman mai goyon bayan Libya ta UNSMIL da MDD ta tura zuwa kasar zuwa ranar 15 ga watan Yunin shekarar nan ta 2016.

Kwamitin ya kuma bayyana cewa, yana goyon bayan yarjejeniyar siyasa ta Libya da aka kulla a watan Disamba na shekarar 2015, yana kuma sa kaimi ga bangarorin daban daban na kasar da abin ya shafa su gudanar da harkokin yarjejeniyar yadda ya kamata.

Bugu da kari, kwamitin sulhun, a nasa bangare ya nuna goyon baya ga tawagar musamman nan da manzon musamman na babban magatakardan MDD dake kula da batun Libya da su taimaka wa kasar Libyar, wajen warware matsalar kasar ta hanyar siyasa.

Kwamitin sulhu na MDD ya yanke shawarar kafa tawagar musamman mai goyon bayan Libya wato UNSMIL a ran 16 ga watan Satumba na shekarar 2011, domin taimakawa kasar samun dauwamamman zaman lafiya, daga bisani ya taba tsawaita wa'adin aikin tawagar sau da dama. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China