Tawagar MDD mai kula da aikin tallafawa kasar Libya ne ya jagoranci taron, wanda ya samu halartar wasu membobin kwamitin shirya kundin tsarin mulkin Libyan 32.
Za a kwashe kwanaki ana gudanar da taron, kuma mahalarta taron za su tattauna wasu batutuwa don cimma matsaya guda a kansu.
Kwamitin ya kunshi membobi 55, sai dai wasu daga cikinsu basu halarci taron ba a wannan karo, sakamakon rashin gamsuwa kan ayyukan da aka tanada wajen shirya kundin tsarin mulkin kasar.
Kwamitin shirya kundin tsarin mulkin na Libya, ya fara gudanar da taronsa na farko a watan Afrilun shekarar 2014, da niyyar samar da daftarin tsarin mulki cikin kwanaki 120, sa'an nan za a gabatarwa jama'ar kasar, domin su kada kuri'ar raba gardama don zartas da kundin.
Amma sakamakon yakin da ya-ki-ci-ya-ki-cinyewa a kasar, har yanzu ba a kammala aikin samar da daftarin kundin tsarin mulki a kasar ba.(Bello Wang)