Jaridar ta ruwaito babban jami'in sojojin kasar Faransa na cewa, Faransa na yakar sansanonin kungiyar IS, amma dole ne ta taka tsan-tsan game da wannan batu.
A cikin labarin, an kuma bayyana cewa, gwamnatin Libya ba za ta amince da kasashen yammacin duniya da su dauki matakan soji a kasar ba, Faransa na dogara kan rundunar soji ta musamman don gudanar da matakan soji a kasar, haka kuma Faransa ta tura jiragen saman yaki don sintiri game da sansanoninn kungiyar IS a kasar Libya.
A watan Nuwambar bara, an kai hare-haren ta'addanci sau da dama a birnin Paris dake kasar Faransa, abun da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da wadanda suka jikkata da dama. Kungiyar IS ta dauki alhakin kai hare-haren, sannan sojojin Faransa sun inganta yaki da kungiyar IS a kasashen Iraqi da Siriya.(Bako)