in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Senegal ta sayi manyan motocin dakon kaya kirar kasar Sin
2016-02-07 12:57:42 cri
A ran 6 ga wata, shugaban kasar Senegal Macky Sall ya halarci bikin mika manyan motoci daukan kaya guda 73 da aka yi a babban dakin wasan kwaikwayo dake birnin Dakar , hedkwatar Senegal.

An mika wadannan motoci ga gwamnatin kasar Senegal, bisa kwagilar da aka kulla a tsakanin gwamnatocin Sin da Senegal, watau cikin shekaru biyar a tsakanin shakarar 2016 zuwa shekarar 2020, gaba daya kungiyar hadin gwiwar kamfanonin sufurin ta kasar Senegal za ta sayi manyan motocin daukan kaya dubu uku, bisa jimillar dallar Amurka miliyan 375.

Dangane da wannan, babban sakataren kungiyar Thierno Diouf ya bayyana cewa, sana'ar jigilar kaya ta zama muhimmin aiki ga kasar Senegal wajen neman ci gaban kasa, da kuma muhimmin matsayi ga kasar Senegal.

Kaza kila, za a canja tsoffin motocin da ake amfani da su da wadannan sabbin motoci, lamarin da za a iya rage yawan kudin da za a kashe wajen jigilar kayayyaki a kasar, yayin da ake kuma kyautata kwarewar sana'ar jigilar kaya a duk fadin kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China