in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ofishin jakadancin Sin dake Senegal ya gudanar da taron manema labaru game da taron FOCAC
2015-11-24 10:34:33 cri
Tun daga ranar 4 zuwa 5 ga watan Disamba, za a gudanar da taron koli na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka ko FOCAC a takaice, a birnin Johannesburg dake kasar Afirka ta Kudu.

Game da hakan, ofishin jakadancin Sin dake kasar Senegal ya gudanar da taron manema labaru a jiya Litinin, inda jakada Zhang Xun na Sin ya yi bayani don gane da taron, yana mai cewa a shekarar 2006, Sin da Afirka sun tsaida wani kuduri na daga matsayin taron ministoci, na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka karo na uku, zuwa taron koli na Sin da Afirka, taron da zai gudana a Johannesburg,wanda kuma zai sa kaimi ga inganta dangantakar dake tsakanin Sin da nahiyar Afirka.

Ya zuwa yanzu, shekaru kimanin 10 sun wuce, Sin da Afirka sun shiga wani sabon mataki na raya tattalin arzikin su, inda Sin ke fuskantar aikin kyautata tsarin tattalin arziki da bunkasa masana'antu, kana kasashen Afirka na fatan za a gaggauta zamanintar da masana'antu da aikin noma.

Game da hakan, Zhang Xun ya bayyana cewa, Sin tana da fifiko a fannonin tattalin arziki, da fasahohi, da albarkatun kwararru, da na'urori da dai sauransu, yayin da kuma take fatan taimakawa kasashen Afirka wajen samun bunkasuwar tattalin arziki mai dorewa.

Ya ce taron koli na dandalin tattaunawa dake tafe a birnin Johannesburg, zai kara inganta dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka, kana kuma taro mai ma'ana a tarihin raya dangantakar sassan biyu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China