Gano wannan iskar gas ya bayyana nasarar da kamfanin Kosmos Energy yake cigaba da samu a wannan yanki, bayan gano wani tarin iskar gas a gabar kasar Mauritania dake makwabtaka da Senegal, a cewar sanarwar.
Kamfanin ya kara da cewa iskar gas din dake karkashin kasa zai iya cimma cuba biliyan 17,000. Bayan wannan iskar gas, kuma wani kamfanin kasar Burtaniya Cairn Energy ya gano man fetur a shekarar 2015 a gabar Senegal, da aka kiyasta cewa a kowa ce rana za a iya hako gangar danyen mai inganci dubu 8, a cewar wani sakamakon gwaje gwaje. (Maman Ada)