in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Senegal: Ana ci gaba da takadama kan rage wa'adin shugaban kasa daga shekaru 7 zuwa shekaru 5
2016-01-12 13:25:23 cri
Shirin shugaban kasar Senegal Macky Sall na rage wa'adinsa na shugaban kasa daga shekarau 7 zuwa shekaru 5, na ci gaba da janyo cece-kuce a fagen siyasar kasar. Bisa zarge-zargen dake fitowa daga masu adawa da shi dake daukar wasu kalamansa na baya bayan nan a matsayin wata niyyar ta karyata maganarsa, shugaban kasar Senegal ya kara daga muryarsa. "An zabe ni ta tsarin demokaradiyya. Ban yi amfani da mamakai ba domin samun mulki. Ban take doka, ko yin magudi wajen samun wannan wa'adi ba. 'Yan kasar Senegal da kansu suka zabe ni. Wadanda suke kokarin sanya mini matsayin lamba, to suna bace wa," in ji Macky Sall. Shugaban Senegal, da ya kai ziyara a ranar Asabar da ta gabata a Louga dake tsakiyar kasar, ya kara da cewa, "Ni ne na dauki wannan mataki na gudanar da gyare-gyare domin idan ana jimawa kan mulki, to sai rika tsammanin kasar take ce ta kai kadai. Dalilin haka ne, na dauki niyyar yin wa'adi biyu." (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China