in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta mika ginin koyarwa na kwalejin Confucius ga Senegal a hukunce
2016-02-04 20:01:32 cri
A jiya Laraba ne, a hukunce aka mika wani ginin koyarwa na kwalejin Confucius a Dakar, babban birnin kasar, ginin da kasar Sin ta taimaka wajen gina shi.

Jakadan kasar Sin dake kasar Senegal Zhang Xun ya bayyana cewa, kwalejin Confucius na jami'ar Dakar ya kasance wata muhimmiyar kafa ga matasan kasar wajen kara fahimtar harkokin kasar Sin da koyon al'adunta.

Ya kuma yi imani cewa, ginin koyarwa da aka gina zai taimaka matuka wajen kyautata yanayin koyarwa na kwalejin Confucius, ta hanyar samar da yanayin mu'amalar al'adu mai kyau a tsakanin Sin da Senegal.

Bugu da kari, jakada Zhang ya ce, a nan gaba, kasar Sin za ta ci gaba da dukufa wajen ciyar da mu'amalar dake tsakanin al'ummomin kasashen biyu gaba, domin karfafa fahimtar juna a tsakanin kasashen biyu, da ba da taimako ga bunkasuwar al'adu da harkar koyarwa a kasar Senegal. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China