Yankin masana'antun za a gina shi a cibiyar birnin Diamniadio mai tazarar kilomita 30 daga birnin Dakar, bisa shirin gyare gyaren birane da ya kunshi gina unguwannin hukumomi, yankunan gidajen jama'a, yankunan masana'antu, jami'o'i da kuma filayen hada hada. A cewar Shugaba Macky Sall, kasar Sin na aiki domin taimakawa Afrika kasancewa cikin cigaban masana'antu. (Maman Ada)