in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashe yammacin Afrika 3 na zaman makoki na kwanaki 3 ga wadanda suka mutu a harin kasar Mali
2015-11-23 13:09:29 cri
Shugaban kasar Senegal Macky Sall da ke ziyara a kasar Mali, ya sanar a jiya Lahadi cewar, shugabannin kasashe mambobin kungiyar raya yankin kogin Senegal wato OMVS sun yanke shawarar gudanar da makoki na kwanaki 3 daga yau Litinin don nuna jimami game da wadanda suka mutu a harin da aka kai a wani otel da ke birnin Bamako hedkwatar kasar Mali.

Sall ya sanar da hakan ne, a yayin taron manema labaru da aka shirya tsakaninsa da takwaransa na kasar Mali Ibrahim Boubacar Keïta, ya ce, shugabannin kasashen kungiyar OMVS da suka hada da shugaban kasar Guinea Alpha Condé, da na Mauritaniya Mohamed Ould Abdel Aziz, gami da shi kansa, sun tsaida kuduri tare, don nuna cewa, wadannan kasashe 3 sun hada gwiwa da jama'ar kasar Mali.

Sall ya ce, game da harin ta'addanci, bai kamata a bar jama'ar kasar Mali su kadai ba, kasar Senegal da sauran kasashe za su yi kokari tare, don tabbatar da dukkan jama'ar da su zabi rayuwarsu, da samun cikakken yanki da mulkin kai na wadannan kasashe.

A nasa bangare, shugaba Keita ya gode wa Sall da ya ziyarci Mali yayin da kasar ke shiga mawuyacin hali. A matsayin shugaban karba-karba na kungiyar ECOWAS, Sall ya ce, za a mayar da batun rigakafi da yaki da ta'addanci ya zama batun da za a tattauna a taron kolin kungiyar mai zuwa.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China