Haka kuma, ya ce, kasar Sin tana amfani da fasahohin zamani wajen gina ababen more rayuwa a nahiyar Afirka, hakan ya sa, an gina kayayyaki masu inganci matuka kuma cikin sauri, lamarin da ya taimaka wa kasashen Afirka matuka wajen samun ababen more rayuwa masu zamani. A halin yanzu kuma, kungiyar AU da kasar Sin suna tattaunawa kan karfafa hadin gwiwa da mu'amalar dake tsakaninsu, domin aiwatar da sakamakon da aka samu cikin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka da aka yi a karshen shekarar da ta gabata a kasar Afika ta Kudu.
Bugu da kari, malam Ibrahim ya nuna cewa, kungiyar AU na gudanar da harkokin jadawalin shekarar 2063 yadda ya kamata, wanda yake mai da hankali kan kyautata yanayin ababen more rayuwa na zamani a kasashen Afirka, domin raya harkokin ciniki da masana'antu na mambobin kungiyar AU, da kuma ciyar da dunkulewar kasashen Afirka gaba yadda ya kamata. (Maryam)