in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan kudin shiga na jama'ar kasar Sin ya fi samun saurin karuwa bisa na GDP a shekarar 2015
2016-01-22 20:21:49 cri

Hukumar kididdiga ta kasar Sin ta ba da kididdiga a ran 19 ga wata cewa, matsakaicin yawan kudin shiga da jama'ar kasar Sin suka samu a shekarar 2015 ya kai kudin Sin RMB 21,966, wanda ya karu da kashi 8.9 cikin dari bisa na makamancin lokaci na 2014. Amma idan an kau da tasirin hauhawar farashin kayayyaki, wannan adadi shi ne kashi 7.4 cikin dari, wato ya fi sauri idan aka kwatanta shi da saurin karuwar GDP na kashi 6.9 cikin dari.

Tun lokacin da aka gabatar da sakamakon binciken da aka yi a birane da yankunan karkara na kasar Sin a farkon watanni uku na shekarar 2014, saurin karuwar matsakaicin yawan kudin shiga da jama'ar kasar Sin ya fi saurin karuwar GDP a kasar a cikin shekaru biyu a jere. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China