in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
GDP a Sin ya karu da kashi 6.9 cikin dari tsakanin Yuli da Satumban bana
2015-10-19 13:55:28 cri

Hukumar kididdigar kasar Sin ta fada a yau Litinin cewar, tattalin arzikin kasar ya karu da kashi 6.9 cikin 100 a watanni uku wato daga watan Yuli zuwa Satumban bana idan aka kwatanta shi da na makamancin lokacin bara, sai dai ya yi kasa idan aka kwatanta da watanni shida na farkon shekarar wanda mizaninsa ya kai kashi 7 cikin 100.

A cewar hukumar kididdigar, a watanni tara na farkon wannan shekara, GDP na Sin ya kai yuwan tiriliyan 48 da digo 78 kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 7 da digo 68, wanda ya karu da kashi 6 da digo 9 idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara.

A watanni 9 na farkon wannan shekara, idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara, yawan kudin da aka samu daga masana'antun kasar Sin ya karu da kashi 6.2 cikin 100, sannan yawan jarin da aka zuba kan kaddarorin gwamnati ya karu zuwa kashi 10.3 cikin 100, yayin da jarin da aka zuba kan gidajen kwana ya karu da kashi 2.6 cikin 100, sai kuma yawan kudin da aka samu daga wajen sayar da kayayyakin yau da kullum ya karu da kashi 10 da digo 3 cikin 100.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China