A shekarar 2014, yawan karuwar GDP na Sin ya kai 7.4%. A cikin rahoton aiki da gwamnatin kasar Sin ta gabatar a wannan shekara kuma, an dasa wannan buri zuwa 7% a bana. Kafin wannan, firaminista Li Keqiang ya bayyana a gun taron manema labaru na manyan taruka biyu na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar cewa, kasar na da karfi wajen tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki yadda ya kamata.
Game da yanayin da ake ciki a fannin tattalin arziki a yanzu kuma, rahoton bankin ADB ya bayyana cewa, a matsayinta na kasar da tattalin arzikinta ya fi karfi a Asiya, watakila Sin za ta ci gaba da kasancewa kasar da ta fi ba da taimako wajen samun karuwar GDP a duniya a shekarar 2015 da 2016. A sa'i daya, bankin ya yi kiyasin cewa, saurin karuwar GDP na Sin zai kai 7% a shekarar 2016 bisa na shekarar 2015.(Fatima)