in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
GDP na Sin ya karu da kashi 7.3 bisa dari daga Yuli zuwa Satumba in an kwatanta da makamancin lokacin bara
2014-10-21 14:34:29 cri

Yau Talata 21 ga wata, hukumar kididdigar kasar Sin ta sanar da cewar, yawan kudin da aka samu daga sarrafa dukiyar kasa wato GDP na Sin ya karu da kashi 7.3 bisa dari daga Yuli zuwa Satumba in an kwatanta da makamancin lokacin bara, duk da cewa, GDP na Sin a bana ya sami tafiyar hawainiya, to amma masu tsara manufofi na gwamnati sun ce, ci gaban bai zarce yadda ake tsammanin zai kasance ba, domin hakan ya yi dai-dai da hasashen kasuwannin.

GDP na Sin daga Yuli zuwa Satumba ya karu da kashi 1.9 bisa dari idan aka kwatanta da na Aprilu zuwa Yunin bana.

A cikin watanni 9 na farkon bana, GDP na Sin ya karu da kashi 7.4 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara, har ya kai yuan trillion 42 wanda ya yi daidai da dalar Amurka trillion 6.84. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China