in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin raya Asiya ya kiyasta cewa yawan karuwar tattalin arzikin kasar Sin a shekarar 2015 zai kai kashi 7.2 cikin 100
2015-03-25 14:59:55 cri

Rahoton hasashe bunkasuwar tattalin arzikin nahiyar Asiya na shekarar 2015 da bankin raya Asiya ya bayar a jiya Talata ya ce, a sakamakon rage saurin bunkasuwar tattalin arziki da kasar Sin ta shirya yi, da yin gyare-gyare kan tattalin arzikinta, saurin karuwar tattalin arzikin kasar Sin na shekarun 2015 da 2016 zai ragu kadan. Bankin ya kiyasta cewa, yawan karuwar GDP na kasar Sin na shekarar 2015 zai kai kashi 7.2 cikin 100.

Bisa halin da kasar Sin ke ciki a fannin tattalin arziki, rahoton bankin raya Asiya ya ce, a matsayin kasa mafi girma a fannin tattalin arziki a nahiyar Asiya, mai yiwuwa ne, kasar Sin za ta kiyaye matsayinta ta wadda ta fi samar da yawan gudummawa ga karuwar jimillar GDP ta duk duniya a shekarun 2015 da 2016. Kana bankin ya kiyasta cewa, saurin karuwar GDP na kasar Sin na shekarar 2016 zai kai kashi 7 cikin 100.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China