Bisa shirin da aka fidda, an ce, gaba daya za a nada ministoci guda 16 dake cikin jam'iyyar dake karkashin jagorancin shugaban kasar Salva Kiir, wadanda za su kula da harkokin tsaron kasa da na sojojin da suka yi ritaya, harkokin shari'a da na tsarin mulkin kasa da dai sauransu. Sannan kuma . Har ila yau ministoci guda 10 dake cikin jam'iyyar dake karkashin jagorancin tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar, su ne za su kula da harkokin man fetur, harkokin cikin gida, albarkatun ruwa da aikin ban ruwa da dai sauransu. Shirin har wa yau ya bayyana cewa, za a zabi ministoci guda biyu dake cikin jam'iyyar dake karkashin jagorancin babban jami'in kasar Pagan Amum, da za su kula da harkokin diflomasiyya da hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa da kuma harkokin sufurin kasar.
Kaza kila, za a zabi ministan dake kula da harkokin majalisar ministocin gwamnati da na aikin noma da hatsi na gwamnatin wucin gadin kasar daga sauran jam'iyyun siyasa. (Maryam)