in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yi gargadi kan duk wani koma baya game da yarjejeniyar zaman lafiya a Sudan ta Kudu
2015-11-30 11:04:40 cri

Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta yi kashedi kan duk wani koma baya game da yarjejeniyar zaman lafiya a Sudan ta Kudu, tare da yin kira ga dukkan bangarorin da rikicin ya shafa da su girmama alkawuransu.

A cikin wata sanarwa da aka bayar a ranar Asabar, Nkosazana Dlamini-Zuma, shugabar kwamitin tarayyar AU ta yi gargadi cewa, yarjejeniyar zaman lafiya na cikin wani hali na rashin tabbas, kuma ta yi kira ga dukkan bangarorin da abin ya shafa da su girmama alkawuransu, da suka hada da tsagaita wuta cikin dogon lokaci.

Zuma ta yi kira ga 'yan tawayen Sudan ta Kudu da su halarci taruka na kwamitin hadin gwiwa na kimanta da sanya ido (JMEC) da kungiyar IGAD ta kafa domin tabbatar da shawarwari tsakanin bangarori masu gaba da juna a kasar Sudan ta Kudu.

A ranar Jumma'ar da ta gabata, kwamitin IMEC ya yi wani taro a birnin Juba, hedkwatar Sudan ta Kudu, amma 'yan tawayen ba su halarci taron ba dalilin ci gaba da yaki.

Kungiyar IGAD ta tsara shirya wani taro a ranar 23 ga watan Nuwamba a Sudan ta Kudu domin tabbatar da lokacin mulkin wucin gadi a kasar, amma aka dage wannan haduwa har zuwa wani lokaci na daban. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China