Shirin kula da harkokin abinci ta MDD (WFP), ya karbi kudin tallafin da gwamnatin Sin ta samar domin tinkarar matsalar karanci abinci a kasar Sudan ta kudu.
Wakilan shirin sun ce sun karbi dalar Amurka miliyan 5, kudaden da za a yi amfani da su wajen sayen hatsi, da wake, da mai, da kuma gishiri domin taimakawa wadanda matsalar ta fi shafa a yankunan kasar Sudan ta kudu. An dai kiyasta cewa, mutane miliyan 3 da dubu dari 9 ne a Sudan ta kudun ke fuskantar karancin abinci.
Jami'i mai kula da harkokin da suka shafi kasar Sudan ta kudu na shirin WFP ya bayyana cewa, taimakon na Sin zai biya bukatun dunbin mutanen dake fama da karancin abinci a kasar. (Lami)