in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar IGAD ta yi kira ga sassan Sudan ta Kudu da su rungumi zaman lafiya
2015-12-24 09:49:24 cri

Kungiyar shuwagabannin kasashen Gabashin Afirka wato IGAD, ta bukaci sassan dake adawa da juna a Sudan ta Kudu, da su gaggauta daukar matakan shawo kan bambance bambancen dake tsakanin su, domin tabbatar da yanayin zaman lafiya da lumana a kasar.

Babban sakataren kungiyar Mahboub Maalim, shi ne ya yi wannan kira a birnin Nairobin kasar Kenya, yayin zantawar sa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua. Mr. Maalim ya ce bai kamata a yi watsi da irin rawar da al'ummar Sudan ta kudu suka taka ba, wajen samun 'yancin kan kasar su.

Maalim ya kuma shidawa Xinhua cewa, yanzu haka wakilan tsagin 'yan tawayen kasar sun fara isa birnin Juba, a wani mataki na yunkurin da ake yi na kafa gwamnatin hadaka. Ya ce gwamnati da 'yan adawa sun amince da bukatar dakatar da baiwa hamate iska, za kuma su ci gaba da daukar matakan kyautata yanayin da kasar ke ciki.

Kungiyar IGAD ce ke jagorantar shiga tsakani a rikicin siyasar Sudan ta kudu, kasar da ke shan fama da rigingimu tun cikin watan Disambar shekarar 2013.

Tuni kuma shugaba Salva Kiir, da tsohon mataimakinsa Riek Machar, suka sanya hannu kan yarjejeniyoyi da dama game da dakatar da bude wuta, sai dai IGAD ta yi kashedin cewa kawo yanzu akwai 'yan kasar da dama dake rike da makamai, lamarin dake barazana ga burin da ake da shi na wanzar da zaman lafiya a kasar.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China