Kamar yadda kafar watsa labaran kasar ta bayyana, tawagar ta bar gabashin kasar inda take da rinjaye zuwa kasar Habasha kafin ta isa zuwa birnin Juba, sai dai an ce tawagar bata kunshi Shugaban ta ba Reik Machar.
A wani bangaren kuma radiyon MDD ta bada rahoton cewa kakakin Shugaban kasar Ateny Wek ya bayyana cewar bangarorin biyu za su zama abokan zaman lafiya ba abokan yaki ba.
Ya kara da cewar al'ummar kasar ta Sudan ta Kudu zasu fahimci cewar zaman lafiya ya samu , wanda wani sabon mafari ne a kasar.
Tawagar 'yan tawayen dai ya kamata su isa birnin Juba tun makonni 4 da suka gabata domin fara aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar da kuma shirin gwamnatin wucin gadi kamar yadda aka tsara a cikin yarjejeniyar amma cigaba da arangama tsakanin bangarorin biyu ya kawo tsaiko.(Fatimah Jibril)