Kudurin dai ya tanaji yiwa dokar kirkirar jahohin kasar sauyi, wadda a yanzu ta bada damar kara yawan jahohin daga 10 zuwa 28. Sabuwar dokar dai ta samu amincewar 'yan majalissa 231 cikin 323.
A cikin watan Oktobar da ya shude ne shugaba Salver Kiir ya gabatar da wannan bukata, kafin daga bisani majalissar zartaswar kasar ta mika ta ga majalissar dokokin kasar.
'Yan majalissar dokokin kasar 37 daga jahohin Central Equatroria, da East Equatoria da West Equatoria ba su halarci zaman kada kuri'un ba. Kaza lika shugaban 'yan adawar kasar Riek Machar, ya yi watsi da wannan kuduri, yana mai cewa hakan ya sabawa yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya da sassan kasar suka cimma, cikin watan Agustar da ya gabata.
Tun dai cikin watan Disambar shekarar 2013 ne Sudan ta Kudu ta auka cikin rigingimun siyasa, wadanda suka rikide zuwa fadan kabilanci. Tashen tashen hankulan kasar sun hallaka dubban fararen hula, tare da raba kusan mutum miliyan daya da dubu dari tara da gidajen su.(Saminu Alhassan)