Kafin tashinsu kuma, an ba sojojin tawagar horo na tsawo watanni biyu domin kara kwarewarsu kan ayyukan kiyaye zaman lafiya, ba da agaji, harba bindigogi da kuma jin harshen Turanci da dai sauransu, haka kuma dukkansu sun saurari jawabin da MDD ta yi musu.
Bisa labarin da aka samu, an ce, tun daga shekarar 2000, ya zuwa yanzu, gaba daya ma'aikatar kiyaye zaman lafiyar jama'a ta kasar Sin ta taba aike da sojojin kiyaye zaman lafiya guda 2305 zuwa yankuna guda 9 da abin ya shafa, da suka hada da East Timor, Bosnia da Herzegovina, Liberia, Sudan da kuma Sudan ta kudu da dai sauran yankunan na kasashen duniya da abin ya shafa. (Maryam)