in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ba za ta ba da katin aikin jarida ga wata yar jaridar Le Nouvel Observateur ta Faransa ba
2015-12-26 17:18:58 cri
A yau Asabar 26 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya fidda bayani dangane da daina baiwa 'yar jarida Ursula Gauthier ta mujallar Le Nouvel Observateur ta kasar Faransa katin aikin jarida dake zaune a birnin Beijing na kasar Sin.

Lu Kang ya ce, a ranar 18 ga watan Nuwamba na shekarar bana, Ursula Gauthier ta samar da wani rahoto a mujallar Le Nouvel Observateur ta kasar Faransa, inda ta nuna goyon baya ga wadanda suka aikata lafuffukan ta'addanci da kuma kashe fararen hula, lamarin da ya tada hankulan jama'ar kasar Sin sosai, shi ya sa a ganin kasar Sin, bai dace da ta ci gaba da yin aiki a nan kasar ba, haka kuma, ya kamata ta nema gafara daga jama'ar kasa ta Sin kan wannan batu.

Bugu da kari, ya ce, a kullum, kasar Sin tana kiyaye ikon kamfanonin dillancin labarai na kasashen waje dake nan kasar Sin da kuma 'yan jaridun su a kasar yadda ya kamata, amma ba za ta lamunci wani ya goyi baya ta'addanci a kasar ba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China