A yau ne hukumar yin kwaskwarima da raya kasar Sin, ofishin yaki da talauci, ma'aikatar kudin kasar, ma'aikatar kula da yankunan kasa da albarkatun kasa da babban bankin kasar Sin suka kaddamar da "shirin sake tsugunar da mutane a wuraren da aka tanada a cikin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 13".
Shirin ya tanadi bukatun da ake da su wajen tsugunar da mutane domin kubutad da su daga talauci, mutanen da suka cancani a tsugunar da su, da yadda za a tsugunar da su, da makamantansu.
Har wa yau shirin zai yi kokarin tsugunar da mutane miliyan 10 a wuraren da suka dace a tsugunar da jama'a. (Tasallah Yuan)