in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane miliyan 100 za su yi fama da talauci a sakamakon sauyin yanayi a cikin shekaru 15 masu zuwa, a cewar bankin duniya
2015-11-09 14:05:02 cri

Bankin duniya ya fidda wani rahoto a jiya Lahadi, wanda ke gargadi da cewa, idan ba a dauki matakan da za su shawo kan matsalar sauyawar yanayi ba, mutane miliyan 100 daga sassan duniya daban daban za su yi fama da talauci a sakamakon tasirin sauyin yanayin nan da shekarar 2030.

Wannan rahoto mai lakabin "dangantaka tsakanin tinkarar sauyawar yanayi da talauci" ya bayyana cewa, matalauta sun fi fuskantar kalubale a sakamakon sauyawar yanayi. Alal misali, tasirin hakan ya hada da rashin samun amfani gona, da hauhawar farashin abinci, da kuma karuwar ciwace-ciwace a sakamakon raguwar ruwan sama, da yanayin zafi da kuma bala'in ambaliyar ruwa da dai sauransu. Lamarin da a cewar rahoton zai fi shafar al'ummun dake nahiyar Afrika, da kudancin Asiya.

Ban da haka kuma, rahoton ya ce, nahiyar Afrika ta fi fama da tasirin sauyin yanayi. Inda ya zuwa shekarar 2030 mai zuwa, mai yiwuwa farashin abinci a nahiyar ya karu da kashi 12 cikin dari, kuma ya zuwa shekarar 2080, karuwar sa za ta iya kaiwa kashi 70 cikin dari a sakamakon sauyin na yanayi.

Rahoton ya kara da cewa, iyalai mafiya talauci dake Afirka na kashe kashi 60 cikin dari na kudadensu wajen sayen abinci, wanda hakan ke sa hauhawar farashin abincin yin mummunan tasiri a gare su.

Bugu da kari, rahoton ya yi kira ga kasashen duniya da su yi kokarin rage fitar da gurbatacciyar iska, ba tare da kara nauyi kan matalauta ba. Kaza lika rahoton ya bayyana bukatar kasashen duniya su taimakawa kasashe mafiya talauci wajen tinkarar wannan matsala ta sauyin yanayi. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China