Jim-Yong ya ce, ziyarar shugaban kasar Sin Xi Jinping a Amurka da halartarsa a taron kolin samun bunkasuwar M.D.D. na da muhimmanci sosai. A yayin taron, za a zartas da shirin samun bunkasuwa bayan shekarar 2015, ciki kuwa babban aikin da ke kan gaba shi ne kawar da talauci. Ya ce Sin ta cimma nasarar taimakawa dunbin mutane don kawar da talauci, kana ta samu fasahohi da dama, saboda haka jawabin da shugaba Xi zai yi kan yadda kasarsa ta cimma nasara a fannin a taron koli na M.D.D. ya zama muhimmi sosai.
Jim-Yong ya ce, zai halarci taron tattaunawa tsakanin kasashe masu tasowa, wanda kasar Sin da M.D.D. za su shirya tare a yayin bikin taron kolin M.D.D.. Ya ce, taron da zai sa kaimi ga kasashe masu tasowa da su more fasahohin da suka samu, abun da ya zama wani muhimmin kashi na ayyukan kawar da talauci da samun wadata a duniya.
Ban da wannan, Jim-Yong ya ce, bankin duniya na maraba da kafa bankin AIIB, kuma yana fatan hadin gwiwa da shi. Ya ce, duk ko wane da ke dora muhimmanci sosai game da batutuwan talauci da na rashin samun daidaito zai yi maraba da kafa wannan banki dake kokarin taimaka wa kasashe masu tasowa wajen raya tattalin arziki da kara samar da guraben aikin yi.
A karshe, Jim-Yong ya ce, yanzu Sin na sauya salon bunkasuwa, yana kokarin karkata hankalinta daga fannonin kirkire-kirkire da fitarwa da zuba jari zuwa ba da hidima, da kashe kudade.(Bako)