in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan matalauta a kauyukan kasar Sin a bara ya ragu da miliyan 12 da dubu 320 bisa na 2013
2015-02-27 10:43:03 cri
Sabbin alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta gabatar a jiya Alhamis, sun nuna cewa, yawan matalauta a kauyukan kasar ta Sin a shekarar 2014 ya kai miliyan 70 da dubu 170, adadin da ya ragu da miliyan 12 da dubu 320 idan an kwatanta da na shekarar 2013. An kuma samu wannan sakamako ne bisa ma'aunin matalauta da aka tsara, wanda ya nuna cewa, mutanen da ba sa samun abin da ya kai Yuan 2300 a shekara guda na cikin matalauta.

Bisa sanarwar tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar Sin ta shekarar 2014 da aka gabatar a wannan rana, an ce, yawan kudin da kowane mutum dake kasar Sin ke samu a shekarar 2014 ya kai RMB 20167, adadin da ya karu da kashi 10.1 cikin dari. Kana yawan farashin kaya na kasar a shekarar ya karu da kashi 8 cikin dari, don haka saurin karuwar GDP na kowane mutum dake kasar ta Sin a shekarar 2014 ya karu da kashi 1.2 cikin dari bisa na 2013. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China