Karuwar yawan al'umma cikin sauri na kara yawan mutanen dake rayuwa cikin tsananin talauci a nahiyar Afrika, in ji bankin duniya a cikin wani sabon rahoto.
Amma duk da haka, karfin bunkasuwar tattalin arziki a Afrika ya taimaka wajen kyautata yanayin kiwon lafiya da ba da ilimi ga al'umma a tsaron shekaru 20 na baya bayan nan, tare da rage kangin talauci sosai a wasu kasashen Afrikar da dama, in ji wannan rahoto.
Rahoton mai taken "Talauci a cikin wata Afrika dake cikin tasowa", ya nuna cewa, mutane miliyan 388, kimanin kashi 43 cikin 100 na al'umma, sun yi rayuwa cikin tsananin talauci a kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara a shekarar 2012, shekara ta baya da a cikinta aka samu wannan kididdiga, kimanin wata raguwa ta mutane miliyan 5 idan aka kwatanta da alkaluman shekarar 2011.
Wannan rahoto ya yi kira da a kyautata fadada hanyoyin auna talauci, kuma ya kara da cewa, gibin dake cikin alkaluma na kawo matsala ga masu fada a ji a fagen siyasa wajen kafa wasu tsare tsare na musammun domin taimakawa al'ummomi masu fama da talauci.
Nasarorin da aka cimma domin kawo karshen talauci daga dukkan fannoni na kasancewa da bambanci daga wata kasa zuwa wata kasa, da kuma nau'in al'ummomi, tare da matsayin cimma nasara marar karfi, da kuma wuyar tashi tsaye wajen neman na kai.
Yake yake da tashe tashen hankali na daga cikin manyan matsalolin dake hana ci gaban tattalin arziki, ko ma da neman lalata nasarori na bunkasuwa da aka samu a wannan nahiyar.
Adadin talauci a wajen al'umma a Afrika, abu ne da ba za a amincewa da shi ba, in ji Makhtar Diop, mataimakin shugaban bankin duniya reshen Afrika. Bisa sabbin muradun bunkasuwa mai karko da aka tsara domin kawo karshen kangin talauci zuwa shekarar 2030, akwai jan aiki sosai da za a yi wajen gaggauta rage talauci, in ji mista Diop. (Maman Ada)