A yayin taron, an fahimci cewa, bayan da aka fara aiwatar da manufofin yin gyare-gyare a cikin gida, da bude kofa ga ketare a nan kasar Sin, gwamnatin kasar Sin karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta dauki dimbin matakan yaki da talauci, matakan da suka taimaka wajen kubutar da mazauna yankunan karkara miliyan dari 7 daga kangin talauci, wato kasar Sin ta samu gagarumar nasarar a fannin yaki da talauci da ke jawo hankulan duniya kwarai da gaske.
Bugu da kari, a yayin taron, hukumar siyasa ta kwamitin tsakiyar JKS ta nemi hukumomin gwamnatin kasar da kananan hukumomi na wurare daban daban da su bullo da sabbin matakan kawar da talauci, alal misali, tallafawa kokarin raya masana'antu da aikin tarbiyya da likitanci, samar da guraban aikin yi, samar da sabbin matsuguna ga wadanda har yanzu suke zaune a wasu yankunan da ke kebe, ta yadda mutane kimanin miliyan 50 wadanda har yanzu suke fama da kangin talauci za su iya fita daga halin talauci, sannan an bukaci hukumomin gwamnati da su ba da inshorar zaman rayuwa mafi kankanta ga wasu mutane fiye da miliyan 20 wadanda suke zaune a yankunan karkara, kuma ba su iya yin aiki ba domin tabbatar da ganin sun fito daga cikin kangin talauci. (Sanusi Chen)