in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan masu fama da talauci ya ragu da miliyan 700 a yankunan karkarar Sin cikin shekaru 36
2015-10-16 20:07:51 cri

Hukumar kididdigar kasar Sin ta ba da labari a kan shafinta na yanar gizo ta Internet a yau Jumma'a 16 ga wata, bayan da kasar ta yi gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje a shekarar 1978, sakamakon saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar da manyan ayyukan yaki da talauci a karkashin shugabancin kasar, ya sa ta samu manyan nasarori a fannin kubutad da mutane daga talauci. A yanzu yawan masu fama da talauci da ke zama a yankunan karkarar kasar ya ragu da miliyan 700 baki daya.

A shekarar 1978, yawan masu fama da talauci ya kai kashi 97.5 cikin dari bisa jimilar mutane mazauna yankunan karkarar kasar, wato miliyan 770 . amma a shekarar 2014 da ta gabata, adadin ya kai miliyan 70 da dubu 170, wanda ya kai kashi 7.2 cikin dari bisa jimilar mazauna yankunan karkara. Wato ke nan yawan masu fama da talauci ya ragu da miliyan 700 a yankunan karkarar Sin daga shekarar 1978 zuwa 2014. A kowace shekara yawan masu fama da talauci yana raguwa da miliyan 19 da dubu 450. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China