Jam'iyyar ANC mai mulki a kasar Afrika ta Kudu a ranar Litinin ta yi maraba da sabon shirin ci gaba mai dorewa na SDGs wanda babban taron MDD karo na 70 ya amince da shi.
Jam'iyyar a ta bakin kakakinta Zizi Kodwa ta ce, ta yi maraba da amincewa da shirin na SDGs da kasashen duniya suka yi, har tare da la'akari da banbancin yanayin da kasashe ke fuskanta, karfinsu da kuma matakin ci gaban da ko wace kasa ta cimma.
Shirin na SDGs ya fitar da sabon tsari don kawo sauyi da ci gaba wanda zai mai da hankali a kan sauraren muryar kasashen da suka fi fama da talauci kuma suke cikin kunci matuka.
SDGs har ila yau yana hade tare da daidaita sassa uku na ci gaba mai dorewa, kamar tattalin arziki, zamantakewar al'umma da kuma muhalli, sannan ya shiga cikin jadawalin shirin ci gaba mai dorewa na shekara ta 2030.(Fatimah)