Wani jami'in gwamnatin kasar Sin ya bayyana kudurin gwamnatin kasarsa na aiki tare da kasar Afirka ta Kudu da ragowar kasashen Afirka na ganin an gudanar da taron kolin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka wato FOCAC a takaice cikin nasara.
Jami'in wucin gadi mai kula da ofishin diplomasiya na kasar Sin da kasar Afirka ta Kudu Li Song ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga wakilan dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka karo na 4 (CATTF) a birnin Pretoria.
Li Song ya ce, kasar Sin na daukar taron kolin na FOCAC a matsayin wata muhimmiyar dama ga shugabannin sassan biyu ta tsara hanyoyin bunkasa hadin gwiwar da ke tsakaninsu zuwa wani sabon matsayi.
Ya kuma bayyana kudurin kasar Sin na yiwa taron kolin duba na gaskiya da adalci, ta yadda zai yi tasiri ga manufofi da kuma muradun sassan biyu. Baya ga bullo da matakan hadin gwiwa tare da tattauna hanyoyin gina layukan dogo, tagwayen hanyoyin zamani, da filayen jiragen sama a Afirka.
Bugu da kari, taron kolin zai yi kokarin kulla hadin gwiwa a bangarorin masana'antu, harkokin kudi, matakan rage talauci, inganta tattalin arziki da kare muhalli. Sauran sassan sun hada da al'adu, musaya tsakanin al'ummomin kasashen biyu, sai kuma hanyoyin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a nahiyar Afirka.
Ana sa ran gudanar da taron kolin na FOCAC ne daga ranar 4 zuwa 5 ga watan Disamba a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu. (Ibrahim)