in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masanin Afrika ta Kudu ya jinjinawa Sin kan alkawarinta na tallafawa shirin muradun ci gaba
2015-09-30 10:18:14 cri

A ranar Talatar nan wani kwararre 'dan kasar Afrika ta Kudu ya yabawa gwamnatin kasar Sin saboda alkawarin da ta yi na samar da kudi har dalar Amurka biliyan 2 domin aiwatar da shirin muradun ci gaba bayan shekarar 2015 a kasashe masu tasowa.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ne ya yi alkawarin samar da makudan kudaden a yayin da ya halarci babban taron MDD kan sha'anin ci gaban kasashen duniya wanda aka yi a farkon wannan mako a birnin New York.

Dr Siphamandla Zondi, wanda shi ne babban daraktan cibiyar tattauna batutuwan duniya na Afrika ta Kudu, ya ce, wannan yunkurin da gwamnatin Sin ta yi lamari ne da zai haifar da gagarumin ci gaba ga kasashe masu tasowa.

Da yake zantawa da kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua, Zondi ya ce, shirin ci gaban muradun karni na MDGs da aka bullo da shi ya taka muhimmiyar rawa, sai dai har yanzu akwai bukatar a sake samar da karin kudade domin ci gaba da aiwatar da shirin.

Ya ce, kasar Sin ta yi rawar gani, ta ba da mamaki, kuma ta zama abin misali yayin da wasu kasashe ke ta surutu tuni Sin ta yi hubbasa domin kawo sauyi a shirin muradun ci gaba bayan shekarar ta 2015.

Zondi ya kara da cewar, al'amurra za su sake rincabewa muddin ba'a samar da kudaden da za'a ci gaba da aiwatar da shirin raya muradun karnin ba a kasashe masu tasowa. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China