Ministan harkokin cikin gida na kasar Afirka ta Kudu Maluci Gigaba ya bukaci kungiyar tarayyar Turai (EU) da ta sake yi wa dokar kungiyar da ta shafi 'yan gudun hijira gyaran fuska don magance matsalar kwararar 'yan gudun hijirar da nahiyar Turai ke fuskanta.
Ministan wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a birnin Cape Town, ya kuma soki wasu kasashen Turai da kokarin rufe kan iyakokinsu, barazanar cinnawa 'yan gudun hijira karnuka, da kuma kafa shingaye maimakon daukar matakan da suka dace na taimakawa bakin hauren.
Minista Gigaba ya jaddada bukatar da ke akwai ta yin tattaunawa da kasashen Afirka da na yankin Gabas ta Tsakiya domin magance matsalar kwararrar 'yan gudun hijirar.
Bayanai na nuna cewa, wasu kasashen yankin Turai sun dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa da na motoci a manyan hanyoyinsu a kokarin magance wannan matsala.
Dubban 'yan gudun hijirar ne dai galibinsu daga kasashen Syria suka nausa zuwa arewacin kasashen Turai a 'yan kwanakin nan, lamarin da ya haifar da babban kalubale ga kasashen na Turai.(Ibrahim)