Wata kididdiga da aka fitar a Talatar nan, ta nuna cewar, alkaluman kashe rayukan jama'a da ake yi a kasar Afirka ta Kudu ya karu cikin shekaru 3.
Yawan kashe kashen rayuka a Afrika ta Kudun ya karu da kashi 4 da digo 6 a shekarar 2014/2015 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.
Wata kididdiga da hukumar lura da aikata miyagun laifuka ta kasar ta fitar ta nuna cewar, kimanin mutane dubu 17 da 805 ne aka hallaka tsakanin ranar 1 ga watan Afrilun shekarar 2014 zuwa 31 ga watan Maris na shekarar nan ta 2015 a Afrika ta Kudun.
Kuma an gabatar da wannan kididdiga ne ga kwamitin majalsar dokokin kasar mai kula da al'amurran 'yan sanda.
Babban kwamishinan 'yan sandan kasar Riah Phiyega ya fada a taron manema labarai cewar, wannan kididdiga ta nuna cewar, akwai jan aiki a gaban 'yan sandan kasar, kuma dole su tashi tsaye domin kawo karshen wannan danyan aiki.
Shi ma ministan 'yan sandan kasar Nathi Nhleko ya bayyana makamancin wannnan bayani, inda ya ce, bata garin 'yan sanda su ne ke haddasa wannan mummnan aiki a kasar.
Kimanin 'yan sanda 686 ne ake tuhuma da hannu wajen aikata wannan muguwar halayya a shekarar da ta gabata.
Nhleko ya kara da cewar, nuna banbanci da kuma yaduwar makamai a hannun jama'a na daga cikin dalilan da suka haddasa faruwar wannan al'amari, duk da cewar 'yan sanda na lalata dubban makamai daga lokaci zuwa lokaci.(Ahmad Fagam)