in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta nemi a taimakawa kasashen yammacin Afirka wajen shawo kan annobar Ebola
2015-01-26 20:26:13 cri
Bisa labarin da hukumar kiwon lafiya da tsara iyali ta kasar Sin ta bayar, an ce, a kwanan baya an shirya taron kwamitin zartaswa na hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa, WHO kan batun annobar Ebola a birnin Geneva na kasar Switzerland. Kasar Sin, wadda mamba ce a kwamitin zartaswa na hukumar, ta halarci taron, inda ta yi kira ga kasashen duniya da su kara yin hadin gwiwa wajen taimakawa kasashen yammacin Afirka yadda za su shawo kan annobar Ebola, da kuma inganta tsarinsu na kiwon lafiya bisa ka'idojin hukumar WHO.

Dr. Margaret Chan, babbar direktar hukumar WHO ta halarci taron, inda ta nuna cewa, wannan annoba ta Ebola ta nuna matsalar rashin ingancin tsarin kiwon lafiya a kasashen yammacin Afirka, lamarin da ya sa hukumar WHO ba ta da isashen karfin shawo kan annobar kamar yadda ya kamata. Ko da yake yanzu yanayin shawo kan annobar ya samu kyautatuwa, amma har yanzu ba a kai ga shawo kan ta baki daya ba.

Don haka Dr. Margaret Chan ta yi kira ga kasashen duniya da su kara yin kokarin kawo karshen annobar cikin hanzari, sannan su taimakawa kasashen Afirka ta yadda za su samar da tsarin kiwon lafiya mai inganci, har ma taimakawa kokarin da hukumar WHO take yi wajen bullo da tsarin tinkarar annobar cikin hanzari. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China