in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya yabawa Tu Youyou game da kyautar Nobel ta likitanci da ta samu
2015-10-06 14:24:15 cri

Faraministan kasar Sin Li Keqiang ya nuna yabo a ranar Litinin ga kwararriya a fannin likitanci ta kasar Sin wacce ta samu kyautar Nobel a wannan fanni.

Kyautar da madam Tu ta samu na nuna daukaka da cigaban kasar Sin ta samu a fannin kimiyya da fasaha, da kuma irin babbar gudunmuwar da maganin gargajiya ta kasar Sin yake bayar wa ga harkokin kiwon lafiya da nuna karfi da daukakar da Sin take samu a dandalin kasa da kasa, kamar yadda faraministan na Sin ya bayyana a cikin wata wasikar taya murna da ya aikawa hukumar kula da maganin gargajiya ta kasar Sin.

Mr. Li Ya yaba wa masanan Sin sosai, musammun ma masu bincike a fannin aikin likita, bisa jajircewa ga aikinsu cikin tsawon lokaci da kuma nasarorin da suka samu.

Haka kuma ya nuna kwarin gwiwa wajen ganin an aiwatar da shirin da gwammati ta bullo da shi game da tattalin arziki dake maida hankali kan kirkire kirkire da neman manyan nasarori a ayyukan kimiyya da fasaha mafi cigaba.

Mataimakiyar faraminista Liu Yandong ta bukaci jami'an kungiyar kimiyya da fasaha ta kasar Sin da na hukumar kula da maganin gargajiya ta kasar da su ziyarci madam Tu a gidanta a ranar Litinin da yamma.

Madam Tu, wacce aka haifa a shekarar 1930, ta raba kyautar Nobel din tare da dan kasar Irland William Campbell da kuma Satoshi Omura dan kasar Japan kan taimakon da suka bayar na gano wata sabuwar hanyar maganin zazzabin cizon sauro, a cewar babban taron Nobel a cibiyar Karokinska dake Suede.

Madam Tu da gano wani nau'in magani dake rage yawan mutanen da ke mutuwa sanadiyar zazzabin cizon sauro (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China