in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya ta gudanar da bikin Turkana na yawon shakatawa na shekarar 2015
2015-08-29 13:43:08 cri

 

Jihar Turkana dake arewa maso yammacin kasar Kenya ta gudanar da bikinta na yawon shakatawa na shekarar 2015, abin da ya jawo hankalin mutane kimanin dubu 15, daga kasashen makwabtaka da ita, ciki hadda Uganda, Habasha, Sudan ta kudu da sauransu.

An ba da labari cewa, tun shekarar 1984, masani mai nazarin al'adun Bil Adam Richard Leakey ya gano kasusuwan halittun zamanin baya na wani dan yaro na Turkana mafi cikakke a duniya, hakan ya sa, aka mai da yankin Turkana daya daga cikin wasu wuraren asalin Bil Adam, tare da shigar da shi cikin takardun sunayen kayayyakin tarihi na duniya na shekarar 2001. An fara gudanar da wannan biki tun daga shekarar 2008, da zummar yin kira ga mazaunannen Turkana da su kiyaye al'adun gargajiya, tare da jawo hankalin masu yawon shakatawa daga kasa da kasa, don ciyar da bunkasuwar tattalin arzikin wurin gaba. (Amina)

1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China