in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Barack Obama: Ya kamata Afrika ta zama muhimmin ginshiki na samun bunkasuwar tattalin arzikin duniya
2015-07-26 14:07:27 cri

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya halarci taron koli karo na shida na kasa da kasa na harkokin masana'antu da aka yi a ran 25 ga wata a birnin Nairobi, inda ya bayyana cewa, Amurka na nuna kyakkyawan fata ga bunkasuwar tattalin arzikin kasashen Afrika, kuma Amurka za ta kafa cibiyar taimakawa mata wajen kafa masana'antu ta uku a kasar Mali don baiwa mata goyon baya a wannan fanni.

A cikin jawabin nasa, Mr Obama ya ce, a matsayin daya daga cikin wasu nahiyoyin da suke samun saurin bunkasuwa, ya kamata Afrika ta zama muhmmin ginshiki wajen samun bunkasuwar tattalin arzikin duniya nan gaba.

Ban da haka kuma, Obama ya sanar da cewa, gwamnatin Amurka za ta yi hadin kai da bankuna, asusu da kungiyoyin nuna jin kai don tattara kudi dala biliyan 1, a kokarin tallafa wa ayyukan kafa kamfanoni a duniya, musamman ma ga mata da matasa a Afrika. Yana mai cewa, Amurka za ta kafa cibiyar taimakawa ma mata wajen kafa masana'antu ta uku a kasar Mali kafin karshen wannan shekara da muke ciki. Ban da wannan cibiyar da za ta kafa, Amurka ta riga ta kafa irin wannan cibiyoyi a Kenya da Zambiya. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China