in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya ta kasance daya daga cikin kasashe masu ci gaban yanar gizo a nahiyar Afirka
2015-06-12 11:16:14 cri
Bisa rahoton da dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya wato WEF ya gabatar a kwanakin baya game da harkokin internet na duniya, an bayyana cewa, cikin jerin kasashe 143 da ke bin tsarin yanar Gizo na zamani ko Internet Readiness, kasar Kenya na matsayi na 86 a duniya, kana ta 6 a nahiyar Afirka.

Rahoton ya yi nuni da cewa, ana bin cikakken tsarin dokoki wajen raya harkar yanar gizo a kasar Kenya, inda aka kayyade ka'idoji a fannonin ciniki da tabbatar da asalin masu sayen kayayyaki a kan internet. Ban da wannan kuma, gwmanatin kasar Kenya ta dora muhimmanci ga bunkasuwar fasahohin sadarwa, inda ta sanya wannan fanni a matsayin daya daga cikin manyan ayyukan da aka tsara don cimma burin shirin raya kasa na shekarar 2030. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China