in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Amurka ya isa Kenya a wata ziyarar aiki ta kwanaki uku
2015-07-25 13:06:34 cri
Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya isa birnin Nairobi a ranar Jumma'a da yamma a wani rangadin aiki na kwanaki uku a kasar Kenya a cikin wani yanayi na tsaurarrun matakan tsaro.

Ya kuma samu tabo a filin saukar jigaren sama na kasa da kasa dake Nairobi daga takwaransa na kasar Kenya Uhuru Kenyatta, tare da sauran mambobin gwamnatin Kenya.

'Yan sanda sun kiyaye tsaron filin jirgin saman da manyan makamai. Domin kare tsaron lafiyar shugaba Obama, 'yan sanda dubu goma aka jibge a muhimman wuraren kasar.

Mun dauki karin matakai dalilin yawaitar hare haren kungiyar Al-Shebaab dake fitowa daga kasar Somaliya da za su iya kawo hatsaniya ga wannan ziayara, in ji wani jami'in 'yan sandan Kenya.

Manyan jami'an tsaron kasar Amurka sun isa birnin Nairobi 'yan makwanni kadan kafin zuwan shugaba Barack Obama.

A birnin Nairobi, mista Obama zai halarci wani dandalin kasa da kasa na masu masana'antu (GES), shirin da Amurka ta kirkiro da kuma ke gudana a karon farko a wata kasar da ke kudu da hamadar Sahara. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China