A jawabinta na karbar kayayyakin da ya gudana a birnin Nairobi, fadar mulkin kasar Kenya babbar sakatariyar majalisar zartarwar kasar mai kula da harkokin muhalli da albarkatun kasa Judi Wakhungu ta ce, gudummawar za ta karfafa hadin gwiwar kasashen biyu na hana safarar namun daji ba bisa ka'ida ba.
Ta kuma kara da cewa, kayayyakin za su karfafa yadda ake sa-ido kan yadda mafarauta ke amfani da muggan makamai wajen farautar namun dajin da ke fuskantar barazanar gusewa daga doron kasa.
Tawagar Sinawa marubutan sun ziyarci wuraren kare namun dajin da ke kasar Kenya ce don ganin an kare manun dajin daga miyagun ayyukan mafarauta.
Kasar Sin dai ta sha taimakawa kasar ta Kenya da dabaru da kayayyakin yaki da namun daji ba bisa ka'ida ba, kuma sassan biyu sun karfafa hadin gwiwa a wannan bangare.(Ibrahim)