in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya na fatan cin gajiya daga sabon layin sufurin sama na kasar Sin
2015-08-07 09:56:59 cri

Kasar Kenya na fatan cin gajiya daga sabon layin sufurin sama, wanda zai hada kasar ta Kenya da birnin Guangzhou na nan kasar Sin, wanda kamfanin jirage na China Southern ya kaddamar a ranar Laraba.

A cewar sakatare mai lura da harkokin yawon shakatawa a majalissar zartaswar kasar Kenya Phyllis Kandie, sufurin fasinjoji sau 3 a kowane sati, wanda kamfanin jirage na China Southern ya fara zuwa birnin Nairobi, zai fadada kasuwar yawon bude ido da gwamnatin Kenyan ke kokarin habakawa.

Kandie wanda ya bayyana hakan yayin bikin murnar kaddamar da sufurin jiragen a jiya Alhamis, ya kara da cewa wannan mataki ya zo gabar da ake matukar bukatar sa, musamman a lokacin da huldar tattalin arziki tsakanin Sin da kasar Kenya ke dada habaka, kana yawan baki Sinawa masu zuwa Kenya yawon shakatawa ke dada karuwa.

Rahotanni sun bayyana cewa jiragen wannan kamfani za su baiwa fasinjoji damar zuwa sassan nahiyar Afirka da dama, karkashin tsarin zirga-zirga tsakanin birnin Guangzhou na kasar Sin da kuma birnin Nairobi na Kenya.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China