A yau ne wani bam din da aka dasa a cikin wata mota ya tashi a wani matsugunin da ke tsakiyar birnin Kabul, hedkwatar kasar Afghanistan, inda fararen hula 8 suka rasa rayukansu, yayin da fiye da dari 4 suka jikkata, yawancinsu mata da kananan yara.
Dangane da lamarin, madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana yau a nan Beijing cewa, da kakkausan murya kasar Sin ta la'anci duk wani harin ta'addanci.
Kasar Sin tana goyon bayan kokarin da gwamnatin Afghanistan ke yi wajen tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a kasar. Kasar Sin tana son hada kai da kasashen duniya wajen taimakawa Afghanistan wajen samun zaman lafiya, kwanciyar hankali da bunkasuwa cikin hanzari. (Tasallah Yuan)