in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na fatan sassa daban daban na Afghanistan za su taimaka wajen kawo sulhu a kasar
2015-06-23 21:08:01 cri

Kasar Sin ta yi tir da harin da'yan kungiyar Taliban suka kai a babban ginin majalisar dokokin kasar Afghanistan har ma ya girgiza ta kwarai.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ne ya bayyana hakan yau a nan birnin Beijing, inda ya ce, kasar Sin na yin allah wadai da duk wani nau'in ayyukan ta'addancin kuma ta kowace hanya.

Ya ce, kasar Sin na mika juyayinta ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon harin, da kuma wadanda suka jikkata. Har wa yau kasar Sin na fatan sassa daban daban na Afghanistan za su yi hangen nesa, su kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasarsu, tare da kara ba da taimako wajen sulhun rikicin siyasar kasar a cikin gida. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China