in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatun wajen Sin da Congo(Kinshasa) sun yi shawarwari karo na farko
2015-07-30 10:18:50 cri

A jiya Laraba ne ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin da ma'aikatar harkokin waje da hadin gwiwar kasa da kasa ta kasar Congo(Kinshasa) suka shirya wani taron shawarwari karo na farko a tsakaninsu, taron da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da takwaransa na kasar Congo(Kinshasa) Raymond Tshibanda N'Tungamulongo suka jagorantar cikin hadin gwiwa.

A yayin taron, Wang Yi ya bayyana cewa, an habaka sabuwar hanyar yin shawawari kan manyan tsare-tsare da kuma kara fahimtar juna a tsakanin Sin da Congo(Kinshasa) ta hanyar kafuwar tsarin musayar ra'ayi a tsakaninsu.

Kasashen biyu dai na da kyakkyawar dama ta inganta ci gaban tattalin arzikinsu cikin hadin gwiwa, kasar Sin sahihiyar kawa ce ga kasar Congo(Kinshawa), wadda za ta ba ta babbar gudummawar da za ta taimaka mata raya sana'o'in zamani da kuma masana'antun kasar Congo(Kinshasa). Haka kuma, kasar Sin na dora muhimmanci ga bunkasuwar dangantakar kasashen biyu cikin dogon lokaci, tana kuma son karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannonin aikin noma, gina muhimman kayayyakin more rayuwa, musayar al'adu, aikin tsaro da zaman lafiya, da kuma harkokin kasa da kasa da dai sauransu, ta yadda hadin gwiwar kasashen biyu za ta kasance abin koyi ga hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka, tare da amfanawa jama'ar kasashen biyu yadda ya kamata.

A nasa bangaren kuma, ministan kasar ta Congo(Kinsasha) Raymond Tshibanda N'Tungamulongo shi ma yana ganin cewa, kafa tsarin musayar nan na da muhmmancin gaske, kuma ya mika godiya matuka dangane da taimakon raya kasa da kasar Sin ta samar wa kasarsa cikin dogon lokaci, kuma yana amince da shawarwarin da minista Wang Yi ya bayar kan yadda za a iya inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, yana kuma fatan ci gaba da karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannonin diflomasiyya, siyasa, tsaro da kuma tattalin arziki. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China