in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya tsawaita wa'adin takunkuminsa ga mayakan 'yan tawayen Congo Kinshasa
2015-01-30 14:33:10 cri
Kwamitin sulhu na MDD ya zartar da wani kuduri na tsawaita wa'adin takunkumin da ya kakabawa mayakan kungiyoyin 'yan tawayen kasar Congo Kinshasa.

Yanzu haka dai sabon wa'adin zai cika ne a ranar 1 ga watan Yulin shekarar 2016.

Bisa tanajin kudurin, an bukaci kasashen duniya da su hana kungiyoyin samun damar mallakar makamai, da basu taimako ko duk wani nau'in horo. Kaza lika an bukaci kasashen duniya da su aiwatar da takunkumin hana yawon shakatawa ko amfani da kudi ga wasu mutane, ko kungiyoyin da kwamitin ya sanyawa takunkumin, bisa rawar da suka taka wajen rura wutar rikici, da haifar da matsala ga kokarin wanzar da zaman lafiya da tsaro a kasar ta Congo Kinshasa.

Haka zalika, kudurin ya yi Allah wadai da sabawa dokokin kasa da kasa, kamar kai hare-hare kan fararen hula, da ma'aikatan kiyaye zaman lafiya, da mayakan kungiyoyin 'yan tawayen kasar ta Congo Kinshasa ke yi, kana ya bukaci 'yan tawayen FDLR, da sojojin Lord's Resistance, da su dakatar da tada zaune tsaye, su kuma kwance damarar yaki. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China